Shugaba Buhari na Jagorantar Taro da Tawagar Tsaro
Yanzun nan muke samun labarin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taro da tawagar tsaron.
Najeriya Ana kyautata zaton tawagar za ta tattauna da Buhari ne kan habaka hanyoyin ragargazar makiya kasar.
Najeriya dai na fuskantar matsalolin tsaro da dama, kama daga yankin Arewa har zuwa Kudancin kasar.
FCT, Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaron kasar nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja, The Nation ta rawaito.
Ana sa ran taron zai tattauna batutuwan da suka shafi dabarun bunkasa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan wajen yaki da ta’addanci da rashin tsaro gaba daya.
Read Also:
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
A gefe gida akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).
Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao suma sun halarci taron.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.
Karin bayani na nan tafe…