Zabin Abdullahi Adamu “Ra’ayinsa ne” Kawai ba APC ba – APC

 

Abuja – APC ta dare kan yunkurin da ake yi na yin magudi a jerin sunayen deliget-deliget na zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa.

Jaridar TheCable ta samu labarin cewa akwai wani jerin sunayen da aka sauya da ake son baiwa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan wanda yana daya daga cikin ‘yan takarar tikitin jam’iyya mai mulki.

A ranar Litinin, Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ce Lawan ne dan takarar jam’iyyar na maslaha.

Hakan dai ya sabawa yarjejeniyar da gwamnonin jam’iyyar APC suka yi na neman a mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudu.

Wasu daga cikin mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) sun hada kai da gwamnonin, inda suka ce zabin Adamu “ra’ayinsa ne” kawai ba APC ba.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa:

“Sakataren kwamitin karramawa, Sanata Gumel, mataimaki na musamman ga Lawan, Orji Kalu, bulalan majalisar dattawa, da Hope Uzodimma, suna aiki don ganin cewa deliget da za su kada kuri’a ga Lawan ne kawai za su shiga dandalin Eagle Square.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here