Shugaba Buhari ya Jajanta wa Shugaban Amurka Kan Mutuwar Powell

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa takwaransa Joe Biden na Amurka kan mutuwar tsohon ministan harkokin waje Colin Powell.

Sanarwar wadda mataimaki na musamman ga Shugaban kan yada labarai Garba Shehu ya fitar, ta bayyana marigayin a matsayin mutun nagari da duniya ta yi alfahari dashi.

Hakama Shugaba Buhari ya bayyana marigayi Powell a matsayin ba’amurike dan asalin Afrika na farko da ya rike mukami mafi girma a harkar tsaron Amurka, kuma ya yi amfani da matsayinsa wurin kulla kyakkyawar hulda da kasashen waje.

Shugaban na Najeriya ya kuma ce duniya ba za ta mance da rawar da Colin Powell ya taka ba wurin yaki da cutar shan inna da kuma takaita yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS a nahiyar Afrika.

Collin Powell ya mutu yau Litinin yana da shekaru 84.

Iyalinsa sun ce ya mutu ne sakamakon kamuwa da cutar corona.

Janar Powell soja ne da ya yi fice a aikinsa wanda ya sa ya zama jigo a gwamnatocin jam’iyyar Republicans da dama, da suka hada da babban mai ba da shawara kan tsaron kasa karkashin mulkin Ronald Regan.

Mista Powell ya kuma rike mukamin hafsan hafsoshin soji da sakataren harkokin wajen Amurka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here