Shugaba Buhari ya Kai Ziyara Maiduguri
Shugaba Muhammadu Buhari na wata ziyara ta kwana ɗaya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Read Also:
Buhari ya isa Maiduguri ne da misalin karfe 11 na safe, inda yake tare da rakiyar manyan jami’an gwamnati.
Shugaban ya samu tarba daga gwamnan jihar Babagana Zulum.
Ana sa ran zai gana da ‘yan kasuwar da suka rasa shagunansu a wata gobara a babbar kasuwar jihar da kuma kaddamar da tashar samar da wutar lantarki.