Shugaba Buhari ya Magantu Kan Kashe-Kashen da Ake a Jahar Plateau

 

Gwamnatin shugaba Buhari ta kai ziyara jahar Filato don tattauna batun kashe-kashen da suke faruwa a jahar.

Shugaba Buhari ya ce sam gwamnatinsa ba za ta tsaya ba har sai ta tabbatar da hukunta masu kashe mutane a jahar.

Ya kuma ce, gwamnati za ta zakulo masu hallaka karya doka da oda sannan ta gurfanar dasu a gaban kuliya.

Plateau – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar cafke mutanen da ke da hannu a kashe-kashen da aka yi a jahar Filato, inji rahoton TheCable.

A cikin watanni uku da suka gabata, hare-hare a sassa daban-daban na jahar sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari.

Buhari, wanda Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya wakilta, a wani zaman tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki a jahar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, ya bukaci tattaunawa mai dorewa don samar da zaman lafiya a Filato.

Ya nemi hadin kan shugabannin gargajiya, na addini da na al’umma don inganta zaman lafiya a jahar, sannan ya kuma yabawa Simon Lalong, gwamnan jahar ta Filato, kan kafa majalisar addinai don dakile matsaloli.

Shugaban ya ce makasudin taron shi ne gina tubalin tattaunawa don saukake fahimta tsakanin kabilu, adalci, da karfafa amincewar mutane.

A cewarsa, dabarun samar da zaman lafiya a jahar “dole ne ya kasance mai girma, fadi, gaskiya da dorewa”.

Buhari ya kuma ba da tabbacin cewa “gwamnati ta dage kan ci gaba da kare dukkan ‘yan kasa masu son zaman lafiya, masu bin doka da al’ummominsu”.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jahar Filato cewa:

“Gwamnati ta kuduri aniyar ci gaba da inganta zaman lafiya, hakuri da addinan juna ta hanyar tattaunawa da shiga tsakani”.

Shugaban ya tabbatar wa mazauna jahar Filato cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa an tura karin jami’an tsaro jahar.

Ya kuma jajantawa gwamna Lalong da mutanen jahar Filato kan kashe-kashen da aka yi kwanan nan, inda ya kwatanta hare-haren a matsayin tsagwaran “rashin imani”.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an hukunta duk mutanen da aka samu da hannu dangane da hare-haren da aka kai kwanan nan a jahar Filato, The Cable ta rawaito.

An kai hare-hare kan mutane da dama a garin Jos, babban birnin jahar Filato, da sauran sassan kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda ya yi sanadiyar kashe-kashen mutane da dama, yayin da wasu mazauna garin da dama suka samu raunuka.

Sakamakon hare-haren da aka kai a Jos wasu gwamnatocin jahohi sun kwashe ‘yan asalin jahohinsu dake karatu daga jahar ta Filato.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here