Matakan Cike Fom ‘Din Nigeria Jubilee Fellows

 

Domin rage zaman banza da kuma samar da ayyukan yi ga matasa, gwamnatin Buhari ta kirkiri shirin samar da aiki.

A halin yanzu, an bude kafar yanar gizo domin fara cike fom na aikin.

Hakazalika, mun tattaro muku abubuwan da ake bukata masu sha’awar neman shiga shirin ya kamata su tanada.

Gwamnatin tarayya ta bude kafar cike fom na shirin Nigeria Jubilee Fellowship, shirin da aka tsara ga matasan da suka kammala NYSC a Najeriya, Premium Times ta rawaito.

An bude kafar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ga masu sha’awar cike fom kuma tsarin zai gudana na makwanni shida, “tsakanin 6 ga Satumba zuwa 20 ga Oktoba, 2021.”

Gidan talabijin na Channels ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin a ranar Talatar makon jiya ya kuma bukaci matasa a Najeriya da su yi hobbasa wajen shiga shirin.

Shirin hadin gwiwa ne na karfafa gwiwar matasa tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Shirin Ci gaban Majalisar Dinkin Duniya (UNDP).

Shirin yana nufin hada kwararrun masu digiri ga damar aiki na cikin gida don nuna kwarewarsu na iya aiki ga ma’aikatu daban-daban da kuma horar dasu ilimi daban-daban na duniya.

A cewar shugaba Buhari:

“Ana sa ran shirin zai samar da sabbin dama ga masu digiri 20,000 a shekara yayin da masu cin gajiyar shirin za su iya inganta damar da aka ba su kuma akwai niyyar sada ‘yan Najeriya da ilimin aiki da dabarun da suka dace na tsawon watanni 12, tare da ko ba tare da kwarewar aiki ba, ta yadda za a hada su da damar samun aikin yi a cikin gida.” Hakanan za a ba da zabi uku ga matasan bayan kammala shirin, wadanda suka hada da ci gaba da aiki da kungiyoyin da suka basu aiki, damar kasuwanci, da dandamali don gasa da samun damar ayyukan yi nan gaba.

Hakanan za a ba da zabi uku ga matasan bayan kammala shirin, wadanda suka hada da ci gaba da aiki da kungiyoyin da suka basu aiki, damar kasuwanci, da dandamali don gasa da samun damar ayyukan yi nan gaba.

Sharuddun shiga shirin

Domin cancantar shiga shirin, mai nema dole ne ya zama dan Najeriya kuma ya kammala digiri (Digiri na farko) daga kowane fannin ilimi kuma ya kammala karatu daga 2017 zuwa sama.

Masu nema dole ne su kammala karatun digiri da akalla karamin makin aji na biyu (2.2) ko sama kuma dole ne su kasance akalla ‘yan shekaru 30.

Dole ne masu neman shiga shirin su kasance ba sa aiki da wata ma’aikata a halin yanzu, kuma su kasance sun kammala bautar kasa (NYSC) ko kuma sun samu takardar dage shirin NYSC a kansu.

Sauran abubuwan da ake bukata sune: masu nema dole ne su nuna sha’awa/jajircewa a cikin aikin da suka zaba sannan kuma su nuna sha’awa/jajircewa don ba da gudummawa ga ci gaban zamantakewar tattalin arzikin Najeriya.

Hakanan dole ne su sami kwarewa wajen sarrafa lokaci da nuna kwarewa kuma suna da kyawawan dabarun magana da rubutu.

Domin samun karin bayani da kuma damar shiga shirin, za ku iya shiga shafin yanar gizo da aka tanada don shirin ta nan https://www.njfp.ng/.

A binciken da Legit.ng ta yi a kafar yanar gizo da gwamnati ta samar don shirin, mun tattaro matakan da ake bi wajen cike fom na shirin.

Ga bayani kamar haka:

1. Sunan farko (Firstname):

Bayan bude shafin yanar gizon, masu sha’awar cike fom din dole ne su fara cike fom din ta hanyar sanya sunayensu na farko.

2. Sunan mahaifa (Surname):

Abu na gaba shine sanya sunan mahaifi, ko sunan ahali.

3. Adireshin yanar gizo na imel (Email):

Sannan, dole ne mutum ya samar da adireshin imel na musamman da ba a taba amfani dashi a kan kafar shirin

4. Kalmar sirri ta budewa (Password):

Mataki na gaba shine kirkirar kalmar sirri na budewa ga adireshin imel na musamman da aka samar.

5. Tabbatar da kalmar sirri ta budewa

Mataki na karshe shine tabbatar da kalmar sirrin budewa da aka kirkira.

Bayan kammala cike fom din, za a aika sakon imel zuwa adireshin imel din da aka bayar. Idan baku samu sakon na imel ba, duba babban fayil dinku mai suna Spam/Junk watakila sakon ya fada can.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here