Shugaba Buhari da Mataimakinsa na Ganawa da Shugabannin Tsaro a Fadar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osibanjo suna cikin ganawa da shugabannin tsaro.

Suna ganawar ne a yau Alhamis, 19 ga watan Agusta a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Ana sa ran za a sanar da shugaban kasar batun halin da ake ciki a yaki da ake da ta’addanci a kasar.

Abuja – A yanzu haka, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin ganawa da manyan hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa dake Abuja, jaridar Punch da PM News suka ruwaito.

Har ila yau a wurin taron akwai Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, ya bayyana cewa a ganawar za a sanar da Shugaban kasar ci gaban da aka samu a yaki da ta’addanci a kasar.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here