Matsalar Tsaro: Ba’a yiwa Najeriya Adalci ba Idan Aka Haɗa ta da Afghanistan – Lai Muhammed

 

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammed, ya tafi kasar Amurka domin ganawa da manyan kafafen watsa labarai na aduniya.

Ministan yace sam ba’a yiwa Najeriya adalci ba idan aka haɗa matsalar tsaron da take ciki da na Afghanistan.

Yace Najeriya ta samu nasarori a yakin da take da yan ta’adda cikin shekaru 6 da suka gabata.

Abuja – Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Muhammed, yace Najeriya ba ta gaza ba kuma ba zata bi sahun Afghanistan ba, inda yan ta’adda suka kwace iko, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a Washington DC ta kasar Amurka yayin fira da kafafen watsa labarai na duniya da suka haɗa da BBC rediyo da talabijin, Bloomberg da Politico.

Ministan yaje kasar Amurka ne domin ganawa da manyan kafafen watsa labarai na duniya a kan nasarorin gwamnatin Buhari da kuma kokarin da take na magance matsalar tsaro.

Da yake zantawa da NAN bayan taronsa da kafafen watsa labarai uku, Muhammed yace ba dai-dai bane a rika alakanta yanayin tsaron Najeriya da na Afghanistan.

Muna samun Nasarori a Najeriya

Ya jaddada cewa Najeriya tana samun nasara kan yan ta’adda kuma ba zata bi sahun Afghanistan ba, inda yan ta’adda suka kwace mulki.

Premium times ta ruwaito Lai Muhammed na cewa:

“Najeriya bata gaza ba kuma ba zata taba gazawa ba. Tabbas muna da kalubale sosai a wasu sassan ƙasa amma hakan ba yana nufin mun gaza bane.”

“Kasar da ta gaza itace kasar da babu muhimman abubuwan rayuwa kuma Najeriya ba ta kai wannan matakin ba.”

Shin Najeriya ta afka cikin yaki?

Muhammed yace Najeriya bata tsunduma cikin yaki ba, inda ya kara da cewa ana amfani da labaran karya wajen kara jefa kasar ciki yanayi a idon duniya.

Ministan yace:

“Idan har abinda ya faru a Afghanistan shine zai cigaba, to kamata yayi a yabawa gwamnatin tarayya saboda yadda ta ɗauki mataki kan rashin tsaro a shekaru 6 da suka gabata.”

“Darasin da muka ɗauka a halin da Afghanistan ta tsinci kanta a yau shine, sama da shekaru 20 da Amurka ta shigo cikin lamarin, ta kashe tiriliyoyin daloli, dubbannin yan Amurka sun mutu, amma cikin makwanni Taliban ta kwace iko.”

“Ya kamata wannan ya zama darasi ga kowace kasa cewa idan kana yaki da matsalar tsaro ko wata kungiya mai tsattsauran ra’ayi, yana da wahala ka shawo kan matsalar.”

“Ya zama wajibi ka kasance a shirye kuma ka yi amfani da duk wasu hanyoyi wajen shawo kan matsalar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here