Kotun Oyo ta ci Tarar Ministan Shari’a N50,000 Kan Batun Hana DSS Kame Igboho

 

Babbar kotu mai zama a Ibadan ta ci tarar ministan shari’a Abubakar Malami tarar N50,000.

An bukaci Malami ya biya kudin ne ga lauyoyin Sunday Igboho bisa wasu dalilai da suka mika.

Hakazalika, Malami ya bukaci kotun da ta janye batun hana DSS kame Sunday Igboho nan kusa.

Oyo – Wata Babbar Kotun Jahar Oyo da ke zama a Ibadan ta tsawaita umurnin da ta bayar na hana hukumar tsaro na farin kaya daga kame dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho, Punch ta ruwaito.

Mai shari’a Ladiran Akintola, wanda ya bayar da umurnin a ranar 4 ga watan Agusta a zaman da aka ci gaba da yi a ranar Laraba ya kuma ba da umarnin Malami ya biya N50,000 kasancewarsa wanda ake kara na farko.

An ba da umarnin biyan kudin daga Malami ne saboda shigar da martaninsa kan karar da Igboho ya shigar a kan lokaci.

Igboho, wanda ya kara yawan lauyoyinsa tare da wasu kwararrun Lauyoyi biyu na Najeriya:

Adekola Olawoye da Oladipo Olasope sun nemi Malami ya biya su N250,000 amma kotu ta ba da umarnin biyan N50,000.

A janye batun hana kame Sunday Igboho

Abubakar Malami, a gaban wata babbar kotun jahar Oyo ya nemi a janye umarnin hana kame Sunday Igboho, da daskare asusun bankinsa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a cigaba da sauraron karar a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, Abdullah Abubakar, lauyan da ke wakiltar AGF, ya sanar da kotun cewa ya shigar da korafi na farko kan lamarin.

Abubakar bai iya motsa bukatar tasa ba, tunda ya shigar batun a kan lokaci.

A cewarsa, jinkirin ya faru ne saboda ba a yi masa bayani kan lamarin ba a lokacin da ya dace. Don haka, ya roki kotu da ta kara masa lokaci.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here