Yadda Nake Lallaba Rayuwata da Ciwon Suga a Shekaru 35 da Suka Gabata – Olusegun Obasanjo

 

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda ciwon suga ya wahala shi.

A cewwarsa, ya dauke shi shekaru 35 yana fama da ciwon suga, amma har yanzu yana nan garau.

Shugaban ya kuma bayya matakan da ya dauka suka taimakeshi wajen sarrafa ciwon na suga.

Abeokuta – Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ba bayyana siriin yadda ya ke lallaba rayuwarsa da ciwon suga a shekaru 35 da suka gabata, yayin da ya ce ciwon ya kashe abokan sa da dama amma shi gashi nan garau, Daily Nigerian ta ruwaito.

Cif Olusegun Obasanjo ya fede biri har wutsiya kan batun a ranar Laraba 18 ga watan Agusta a wani bikin da ya halarta na rufe taron ci gaban yara masu ciwon suga na jahar Ogun da aka gudanar a Abeokuta ta jahar ta Ogun.

Taron wanda Cibiyar Ciwon suga ta Talabi ta shirya, ya koyar da yara 21 da ke fama da ciwon suga mataki na 1 a jahar kan yadda ake fama da cutar.

A wani rahoto da Daily Trust ta rahoto, Obasanjo ya ja hankali da kuma shawartar yara da su kula da cutar suga matuka ta hanyar kiyaye salon rayuwa, yana mai cewa ciwon suga ba cuta ne da bai kai wa ga halaka.

Tsohon shugaban ya zayyana wa yaran cewa, lallai su guji shan suga da ma abinci mai dauke da sinadarin carbohydrate sananna a kullum su tabbatar sun rika yin alluran insulin domin kula da cutar da kyau sosai.

Jawabin da Obasanjo ya yi

A wani yanki na jawabin da ya yayi, ya ce:

“An gano ina dauke da ciwon suga sama da shekaru 35 kenan kuma ga ni nan garau, har yanzu ina tafiya, har yanzu ina tsalle-tsalle sama da kasa, har yanzu ina yin abubuwa da yawa mutane da yawa a shekaruna ba za su iya ba.

“Daga lokacin da aka gano ina dauke da ciwon suga, da dama cikin abokaina sun rasu kuma dalilin kenan ba sa kula da ciwon suga yadda ya kamata su kula shi ba.

“Ba komai ko don mutan mataki na daya ne ko kuma na biyu ba, ya zuwa yanzu babu maganin ciwon suga, watakila za a sami magani kafin in mutu, amma ina addu’ar a sami magani kafin ku mutu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here