‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Najeriya 7 a Jahar Katsina

 

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina.

Miyagun sun kashe sojojin Najeriya bakwai bayan da sojojin suka bi sahun ‘yan fashi da suka sace dabbobi sannan suka tsallaka zuwa iyakar Najeriya.

Wani ganau ya ce tun bayan harin da aka kai a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, ba a ga wasu daga cikin sojojin ba.

Jibia, Katsina – Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya bakwai a karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kai harin ne a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, a kauyen Kadobe kimanin kilomita 4 daga kauyen Kukar Babangida.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun hango sojojin Najeriya suna tafe bayansu sannan kuma suka kashe bakwai, The News Wire ta ruwaito.

Da yake ci gaba da magana, mazaunin garin ya bayyana cewa ba a ga wasu daga cikin sojojin cikin ba ciki har da wadanda suka yi kira da a kara musu karfi tun bayan harin.

Mazauna garuruwan da ke kan iyaka a yankunan da ‘yan ta’adda suke sun dogara da sojojin Najeriya don basu agaji lokacin da ‘yan bindiga suka kai musu hari.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here