Shugaba Buhari ya Taya Rochas Okorocha Murnar Cika Shekaru 59 a Duniya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Rochas Okorocha murnar cika shekaru 59 a duniya.
Shugaban kasar ya yabawa Okorocha da irin namijin aikin da yake yiwa kasa da ‘yan Najeriya baki daya.
Ya kuma yabawa Gidauniyar Okorocha wacce a cewar Buhari take taimakon kowa ba nuna bambanci.
Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 21 ga watan Satumba ya aike da sakon taya murna ga tsohon gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha, kan cikarsa shekaru 59 a duniya.
A cikin wani sako ta hannun mai taimakawa shugaban kasa a fannin yada labarai, Shehu Garba, shugaban ya jinjinawa Okorocha kan salon jagoranci mai hangen nesa da ci gaban da yake kawowa a fannoni daban-daban, inji rahoton The Nation.
Read Also:
Shugaba Buhari a cikin sakon da PM News ya ce ya gani ya lura cewa wannan ranar ta tunawa da haihuwar Okorocha ta zo da tarin samun nasarori, mafi mahimmancin gudummawar da ya bayar wajen gina kasa.
Buhari ya ce:
“Na bibiya, tare da mayar da hankali, salon jagoranci na hangen nesa, halayen siyasa da kokarin kawo ci gaba, a cikin kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati, kuma na lura da kwazon ka na gwagwarmaya ko yaushe don jin dadin marasa galihu.
“Ina yaba wa Gidauniyar Rochas, kungiyarka ta agaji, wacce ke ci gaba da karfafa gwiwa da taimakon jama’a a fadin kasar, ba tare da nuna bambancin launin fata, addini ko siyasa ba.
“A ranar cika shekaru 59 da haihuwarka, ina tare da membobin jam’iyyarmu, All Progressives Congress (APC), don yi maka fatan alheri kan tafarkin ka na hidima ga kasa da bil’adama.”