‘Yan Bindiga za su Fara Shiga Gonakan Mutane Suna Girbe Shukan da Manoma Suka yi – Gwamna Masari

 

 

Gwamnan jahar Katsina ya yi gargadin cewa, yunwa ta addabi ‘yan bindiga don haka a kula.

A cewarsa, ‘yan bindiga za su fara shiga gonakan mutane suna girbe shukan da manoma suka yi.

Ya bayyana haka ne a jiya Talata yayin wani taro da aka yi a jahar kan batutuwa da suka shafi tsaro.

Katsina – Gwamna Aminu Masari na jahar Katsina ya yi gargadin a kula game da komawar ‘yan bindigan da yunwa ta fatattaka, zuwa garuruwa da yankuna don satar kayayyakin gona kafin lokacin girbi, Daily Nigerian ta rawaito.

Gwamnan ya yi gargadin ne a ranar Talata 21 ga watan Satumba, a Katsina, a wani taron shawari da ya yi da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed kan yanayin tsaro a jahar.

Taron ya samu halartar Shugabannin hukumomin tsaro na jahar, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da na addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar Masari:

“Saboda yunwa, ‘yan bindiga suna tafiya zuwa al’ummomin da ke kusa da yankin dajin da suke ciki. Sun san cewa lokacin girbi na gabatowa kuma shirin su shine girbe amfanin gona da sace kayan abinci da manoma suka shuka.”

Matakan gwamnati na aiki wajen fatattakar ‘yan bindiga

A baya cikin rahoton TheCable, ‘yan bindiga sun koma tambayar kayayyakin abinci a madadin kudin fansa sakamakon matsayin lamba da suka samu daga jami’an tsaro a jahohi.

Gwamnan ya ce an fatattaki ‘yan ta’adda a cikin jaharsa sakamakon matakan da aka sanya, gami da dakatar da hanyoyin sadarwa na wayar salula da hana sayar da albarkatun mai a gidajen mai da yawa.

Ya umarci shuwagabannin tsaro, da su farka daga bacci tare da addabar masu laifi, hadi da jaddada matsayinsa na cewa ba zai tattauna da ‘yan bindiga ba.

Gwamna Masari ya bayyana cewa jahohin da aka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga sun yanke shawarar daukar mafarauta da ‘yan banga 3,000 wadanda ‘yan sanda za su horar da su don kare mazauna garuruwa.

Ya ce Katsina za ta dauki mafarauta 500 da ‘yan banga – 250 kowanne daga Katsina da masarautar Daura don kare al’ummomi daga hare-haren ‘yan bindiga.

Ya kuma yi bayanin cewa mafarautan da ’yan bangan za su kasance cikin mazauna dindindin don kare mutane da dukiyoyinsu.

Musamman, ya ce, bayan kokarin sojoji, mafarauta da ‘yan banga za su ci gaba da kare al’ummomin, tare da yaba hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da aka tura jahar wadanda, yace sun taimaka wa nasarorin da aka samu a kan ‘yan bindiga.

Mai martaba sarkin Katsina, Kabir Usman, ya yabawa gwamnan kan sabbin dabaru na dakile rashin tsaro a jahar.

Basaraken, wanda ya ce yana adawa da tattaunawa da ‘yan bindiga, ya yi kira ga ministan da ya ci gaba da samar da ingantaccen bayani kan yaki da rashin tsaro a kasar.

Sarkin, wanda ya ki amincewa da tattaunawa da ‘yan bindiga, tare da biyan kudin fansa, ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen yaki da masu laifi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here