‘Yan Bindiga Sun Harbe Mayakan Taliban 2

 

Rahotanni daga gabashin Afganistan na cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe mayakan Taliban biyu da wani farar hula.

Shaidun sun ce mutanen da ke dauke da makamai sun kai hari kan shingen binciken jami’an tsaro a Jalalabad a Lardin Nangarhar.

Kungiyar Taliban ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce duk wadanda suka mutu fararen hula ne.

A ranar Asabar, akalla mutane biyu sun mutu a wani harin bam da aka dasa a gefen hanya a Jalalabad sannan biyu sun jikkata sakamakon fashewar wani abu a Kabul babban birnin kasar.

Lardin Nangarhar tushe ne ga kungiyar masu da’awar kafa daular Islama wato IS wacce ta yi tir da sabuwar gwamnatin ta Taliban.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here