Buhari: Raba Kyautar Mitar Wutar Lantarki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sharewa ‘yan Najeriya kukansu.

A cewarsa, zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin ‘yan Najeriya sun daina biyan haraji.

Ya ce zai tabbatar kudin wutar lantarkin da suka sha kadai za su biya Shugaban kasa ya ce kowa ya kwantar da hankalinsa, don yanzu haka yana fafutukar ganin cewa ‘yan Najeriya sun biya kudin wutar da suka sha kawai, ba tare da wani haraji na daban ba.

Shugaba Buhari yayi wannan alkawarin ne ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, a ranar Laraba.

A cewarsa, yanzu haka gwamnatin tarayya tana kokarin tattara kudaden da za ta samar da mitoci miliyan daya kafin ta samu damar hada mitoci miliyan 6.5 a Najeriya gaba daya.

Kamar yadda Buhari ya wallafa, “A karkashin tsarin shugaban kasa na samar da wuta mita miliyan 1 ba tare da amsar ko sisi daga hannun al’umma ba, yanzu haka an fara kaddamar da shirin a Kano, Kaduna, Legas da Abuja.

“Tsarin da za a sake kaddamarwa zai shafi akalla mutane miliyan 30, don za a yi amfani da mita 6.5 don ‘yan Najeriya su amfana.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here