Dalilin Rashin Samun Damar Ganawa da Gwamnoni- Buhari
Muhammadu Buhari ya bayyana abin da ya hana shi zuwa Jihar Ribas jiya.
An shirya cewa shugaban kasar zai gana da shugabannin yankin Neja-Delta.
A karshe dole aka fasa zaman inda shugaban kasar ya gana da hasfun tsaro A ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, 2020, fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ta yi nadamar rashin ganawa da duk gwamnonin Kudu maso kudu.
An tsara cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi taro da gwamnonin yankin Kudu maso kudu a garin Fatakwal, amma a karshe Ubangiji bai nufa ba.
Shugaban kasar ya ce wani taron gaggawa da ya shiga tare da shugabannin majalisar tsaro ya sabbaba rashin halartar zamansa da gwamnonin kasar.
Read Also:
Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bada uzuri na kin halartar zama da Gwamnonin, jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.
Shugaban kasar ya ce taro ne ya fado masa kwatsam a fadar Aso Rock Villa a kan harkar tsaro. Mai girma Muhammadu Buhari ya ce za a sake samun rana ta musamman da za a rama wannan zama.
Za a sa ranan ne bayan la’akari da wasu batutuwa. Gwamnoni da shugabannin yankin Kudu maso kudu sun bukaci shugaban kasar ya fito gaban Duniya ya ba su hakuri na bata masu lokaci da aka yi a banza.
Garba Shehu ya ce har tawagar shugaban kasar ta fara shirin tafiya Fatakwal, sai aka dakatar da ita, saboda taron gaggawar da Buhari ya shiga a fadar Aso Villa.
“Har ila yau, an yi nadamar dage wannan zama bayan abin ya zama dole.” Inji Garba Shehu.