Zamfara: Gwamnatin Bata da Iko Aka Gwal din Jahar – Nurudden Isa

An samu barkewar cece-kuce bayan gwamnatin Zamfara ta sanar da cewa za ta fara cinikayyar gwal din da aka gano a jihar.

Gwamnonin kudancin Najeriya sun nemi ba’asi a kan dalilin da zai sa Zamfara ta siyar da gwal dinta amma Delta ba zata sayar da man fetur din jihar ba.

Dakta Nurudden Isa, Kwamishina mai kula da albarkatun kasa a Zamfara, ya ce arzikin gwal din ba na gwamnati bane Kwamishina mai kula da albarkatun kasa a jihar Zamfara, Dakta Nurudden Isa, ya ce arzikin gwal din Zamfara ba mallakar gwamnati bane.

Dakta Isa ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa ranar Laraba a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

A cewarsa; “gwamnatin jiha ba ta mallaki ko takun kafa na fili a wurin da ake hakar gwal ba.”

Kwamishinan ya kafe a kan cewa gwamnati na sayen gwal din ne daga hannun masu hakarsa domin hana ficewa da shi daga cikin Najeriya ko Kuma a siyarwa ‘yan bindiga dadi.

“Ita gwamnatin jiha ta na siya ne kawai domin tabbatar da cewa bai shiga hannun batagari da zasu siyar da shi domin siyen makamai ba.

Kazalika, kwamishinan ya kara da cewa gwamnati jihar Zamfara ta haramta hakar gwal tare da fadin cewa “duk mai son shiga kasuwancin hakar gwal sai ya samu izini daga gwamnatin tarayya.”

Kwamishinan ya kara da cewa albarkatun karkashin kasa mallakar gwamnatin tarayya ne kuma ita kadai keda ikon bayar da lasisi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here