Yanda Wata Gobara ta Tashi a Wani Gidan Man Fetur da Kasuwa

Gobara ta tashi a wani gidan man fetur a Jihar Oyo da kuma kasuwa Katako a Jihar Plateau.

An shawarci mutane da su kara lura a lokacin sanyi don kauracewa annobar gobara.

Gwamnati tayi alkawarin kafa kwamitin da zai duba musabbabin gobarar tare da alkawarin tallafawa wanda suka yi asara.

An ruwaito cewa wata babbar tankar man fetur ce ta kama da wuta dai dai lokacin da take juye mai a wani gidan mai da ke yankin Oluwole, Iseyin Saki a Jihar Oyo.

Kafin zuwan yan kwana kwana, ma’aikatan gidan man da makwabta suka yi bakin kokarin don shawo kan wutar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kwamandan yan kwana kwanan jihar Oyo, Mr Moshood Adewuyi, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce ba’a samu mutuwa ko rauni ba.

“Gobarar ta tashi da misalin karfe 6:00 na yamma ranar Litinin dai dai lokacin da tankar mai ke juye mai.

Mun gode Allah da ya kasance da nisa tsakanin famfon mai, kusan mita 400 daga inda lamarin ya faru.

Rumfar gidan man da ofis da kuma harabar gidan man sun tabu,” a cewarsa.

A wani labarin, kayayyakin miliyoyin Naira sun lalace bayan da wuta ta kama akalla shaguna 30 a kasuwar Shasha da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Shugaban yan kwana kwanan, Adewuyi, ya ce jami’an sa sun samu rahoto da misalin karfe 4:25 na asuba ranar Talata.

“Kusan shaguna 30 ne suka kone. Mun samu labarin cewa lamarin ya faru ne sakamakon gyara wutar lantarki da akayi ranar Talata.

Shasha kasuwar kayan marmari da ganyayyaki ce, to kwandunan da aka tare ne suka ta’azzara wutar,” a cewar sa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here