Wasu Batagari Sun Lalata Kotun da Ake Shari’ar Masarautar Zazzau

An fasa ofishin babban alkalin kotun da ake shari’ar masarautar Zazzau a Sabon Gari.

Ita ce kotun da ake shari’a tsakanin sabon sarki Ahmed Bamalli da Iyan Zazzau, Bashir Aminu.

A daren talata ne wasu bata-gari suka shiga, inda suka lalata takardun kotun da sauran abubuwa.

A daren Talata ne wasu bata-gari da ba a san ko su wanene ba, suka fasa ofishin babban Alkalin kotun Dogarawa, Mai Shari’a Kabir Dabo, wanda yake shari’a tsakanin sabon sarki, Ahmed Bamalli da Iyan Zazzau, Bashir Aminu.

Sai da bata-garin suka fasa kotun, tukunna suka samu damar shiga har ofishin babban alkalin.

Bata-garin sun yi kaca-kaca da wasu takardu, sun kuma kwashe kayan da alkalin yake amfani da su idan zai zauna a kotu, da wasu abubuwa da har yanzu ba a gama tantancewa ba.

Wakilin jaridar Aminiya ya bukaci tattaunawa da magatakardan kotun, mai suna Jafaru, amma abin ya ci tura, inda ya ce yanzu dai ba zai iya magana da shi ba, har sai ya tuntubi mai gidansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here