Shugaba Buhari ya Mika Sakon Ta’aziyya Na Rashin Nafisatu Galadima Aminu Usman
Allah ya yi wa Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman rasuwa, kamar yadda sanarwa daga fadar shugaban kasa ta nuna.
Marigayiya Hajiya Nafisa ta kasance babbar aminiya ga iyalin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Hajiya Nafisa mata ce wurin Laftanal Kanal IG USman (mai ritaya) babban dogarin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da uwargidansa, Aisha Buhari, sun yi alhini tare da juyayin mutuwar wata mai kusanci da su, Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman.
Read Also:
Marigayiya Nafisatu mata ce wurin Laftanar Kanal IG Usman, dogarin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari.
A cikin sakon da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga gidan sarautar Adamawa, gwamnatin jiha da kuma jama’ar jahar baki daya.
Shugaba Buhari ya bayyana; “tsananin alhini da tausayawa a sakonsa na ta’aziyya” tare da bayyana Hajiya Nafisatu “a matsayin mace mai amana da bata taba nuna gajiyawa ba wajen bayar da goyon baya ga iyalin shugaban kasa.”
Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya jikanta ya kuma cigaba da tallafawa iyalinta da ta mutu ta bari, kamar yadda Garba Shehu ya sanar.