Shugaba Buhari ya Sauke Shugaban NDE

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauke Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungun, shugaban NDE daga mukaminsa.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

Shugaba Buhari ya umurci karamin ministan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma’aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Wani sashi na sanarwar ta ce, “Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungun daga mukaminsa a shugaban hukumar daukan ma’aikata. Umurnin da aka bada a ranar Juma’a 4 ga watan Disambar 2020, zai fara aiki ne daga ranar Ltinin, 7 ga watan Nuwamban 2020.

“A yanzu, an umurni ministan da hukumar ke karkashinsa, karamin ministan kwadago da ayyuka da zabi shugaban riko daga cikin manyan direktoci da suka cancanta su maye gurbin Dakta Argungun kafin Shugaban kasa ya nada sabo.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here