Najeriya: Shugaban Kasar ya yi Ta’aziyyar Mutuwar Igwe Alex Nwokedi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar rasuwar Igwe Alex Nwokedi, Uthoko na Achalla.

Marigayi Igwe Alex Nwokedi shine basaraken garin Achalla da ke jihar Anambra kuma ya rike mukamai da dama kafin rasuwarsa – Shugaban kasar ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin ya kuma bawa iyalansa da sauran wadanda ya bari hakurin jure rashinsa.

Shugaba Muhammad Buhari ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan gidan sarautan Uthoko Na Eze bisa rasuwar Igwe Alex Nwokedi, Uthoko na Achalla. Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya isa da sakon cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Buhari ya kuma yi wa al’ummar Achalla da majalisar Igwe na Achalla da gwamnatin jihar Anambra ta’aziyya bisa rasuwar basaraken.

Mr Nwokedi shine tsohon shugaban Majalisar Masu Sarautun Gargajiya na Jihar Anambra kuma tsohon shugaban Majalisar Masu Sarautun Gargajiya na Jihohin Kudu guda tara.

Ya kuma rike mukamin Manaja, Na sashin hulda da Jama’a ta NNPC kuma shine sakataren watsa labarai na Janar Olusegun Obasanjo a lokacin yana shugaban kasa na mulkin soja daga 1967 zuwa 1979.

Shugaba Buhari ya ce Igwe Nwokedi ya aikata muhimman abubuwa da tarihi ba za ta manta da shi ba ya kuma yi adduar Allah ya gafarta masa ya kuma bawa wadanda ya bari a baya hakurin jure rashinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here