Sarkin Calabar: Kawai ka Sauka Daga Mulki ka Gaza- Gwamnan Cross River

Irin ta Kano, Sarkin gargajiyan jihar Cross River ya yi fito-na-fito da gwamnan.

Ya ce gwamnan ya daina daukar wayansa kuma ba ya kiransa – Ya zargi gwamnan da rashin iya mulki da gudanar da al’ummar Mai Martaba Obong na Calabar, Edidem Ekpo Okon Abasi Otu, ya daura laifin sace-sace da fashe-fashen da akayi a jihar Cross River makon da ya gabata kan gwamna Ben Ayade, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi kira ga gwamnan ya sauka daga mulki domin baiwa gwamnatin rikon kwarya daman gyara kuma ya natsu ya dauki darasin yadda ake mulki da tafiyar da al’umma. Sarkin wanda yayi jawabin lokacin da ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar, Liyel Imoke, ya ce an kai hare-haren ne saboda gwamnan ya daina shirya zaman hukumomin tsaro.

“Ya daina shirya zaman hukumomin tsaro. Da ya kira jami’an tsaro, ya zauna da su bayan samun labarin abinda ya faru a Legas da wasu wurare, da hakan bai faru ba, ” yace. Sarkin ya ce gwamna Ayade ba ya daukan wayansa idan ya kirashi.

Ya yi kira da gwamna ya canza dabi’unsa saboda kowani mai ruwa da tsaki a jihar na da hakkin ganin shugabansu. Sarkin gargajiyan ya bayyanawa tsohon gwamnan cewa ya fadawa Ayade jihar ba zata cigaba ba idan ya cigaba da mulki haka. “Mu fadi gaskiya, mu daina boye-boye; ba za mu iya cigaba da rayuwa haka ba. Ka fada mai akwai bukatar sulhu,” ya ce.

Amma daya daga cikin masu magana da yawun gwamnan, , Christian Ita, ya ce gaskiya da kamar wuya a ce maigidansa yaki daukan wayar Sarkin. Ya ce gwamnan na ganin girman Obong sosai a matsayinsa na uban kowa a jihar. “Bai dace yayi kira ga gwamnan wanda yake iyakan kokarinsa wajen kawo cigaba jihar yayi murabus ba,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here