Sarkin Musulmai: Wawusan Kayan Tallafin Korona Bai Hallata ba

Sarki Musulmi ya yi Alla-wadai da irin sace-sacen kayan abincin da aka yi a Najeriya.

Sultan ya ce ya zama wajibi masu fada aji su fito suyi magana kan lamarin – Ya yabawa matasan arewa bisa rashin biyewa sauran mutane wajen yin hakan.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya siffanta wawusan kayan tallafi, sace-sace da lalata ma’aikatun gwamnati a matsayin zalunci da mugunta Sarkin wanda yayi jawabi a taron murnar cikar Arewa House shekaru 50, ya jinjinawa matasan Arewa bisa biyayyan da suka yiwa shugabanni, rahoton Daily Trust.

Ya ce talauci ba uzuri bane da zai sa a rika lalata dukiyoyin kasa. Yace: “Mun san akwai talauci amma talauci ba uzuri bane na yin mugunta.”

“Saboda abinda ya faru a kwanakin nan mugunta wasu wasu bata gari sukayi kuma ina ganin akwai bukatar muyi Alla-wadai da hakan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here