Ondo: Wasu Mutune Sun Mutu Sakamakon Trela da ta Afka Musu a Kasuwa

Trela ta kubce wa direba ta faɗa cikin kasuwa ta kashe mutum 10.

Hatsarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba a jihar Ondo – Wadanda abin ya faru a idonsu sun ce birke ce ta dena aiki hakan yasa motar da ƙwace wa direban Aƙalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a yammacin ranar Asabar a kasuwar Akungba ta Jihar Ondo.

An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata trela da ƙwace wa direban ta kutsa cikin kasuwar Akungba ta take mutum 10 har lahira tare da raunata wasu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shaidun ganin ido sun bayyana cewa birkin trelan ne ya samu matsala.
“Trelan na saukowa daga Dutsen Okerigo da ke kusa da Jami’ar Adekunle Ajasin ne a lokacin da ta kwace wa direban saboda rashin birki,” a cewar majiyar. Amma majiya daga rundunar ƴan sandan jihar ta ce mutum takwas ne suka mutu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here