Shugaba Buhari na Tafiyar Hawainiya – Hakeem Baba Ahmed

 

Kungiyar Dattawan Arewa ta soki Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar kakakin kungiyar, shugaban kasar na tafiyar hawainiya sosai wajen magance wasu matsalolin kasar.

Ya ce zai fada wa Buhari cewa kasar na rugujewa idan ya samu damar tattaunawa da shi A wani abin da zai haifar da martani daban-daban daga ‘yan Nigeria, an nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar mataki kafin abubuwa su tabarbare sosai a kasar.

Kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed ne ya yi kiran. A cewarsa, Shugaba Muhammadu Buhari na tafiyar hawainiya sosai.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, 24 ga Maris. Da yake ci gaba da magana, ya ce zai fada wa shugaban kasar zuciyarsa idan ya samu damar zama da shi.

Ya ce zai fada wa shugaban kasar ya farka ga nauyin da ke kansa kasancewar kasar ta dauki hanyar rugujewa.

Ya ce: “Idan na samu damar tattaunawa da shugaban kasar, zan ce: ‘Yallabai, don Allah ka farka ka fuskanci zahiri, ƙasar nan tana wargajewa.”

“Me yasa bamu da tsaro? Me ya sa ’yan Najeriya ba za su magance matsalar ta’addanci da satar mutane ba? Wadannan abubuwan biyu, shekaru uku da suka gabata babu su. Shin wani yana yin waɗannan tambayoyin? Shin kuna da wannan jituwa a cikin hukumomin tsaron ku? Shin kuna da hanyar gano hakan saboda bamu da lokacin da zaka gyara kasar nan a lokacin da ka dama kuma a yanda kake tafiya, kana jinkiri sosai kuma mutane sun fara yanke kauna da gwamnatin ka kuma wannan shine dalilin da ya sa ka ga mutane na fadin cewa ba ma son kasancewa cikin Najeriya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here