Akwai Alaka Mai Karfi Tsakanin Shugaba Buhari da Bola Tinubu – Garba Shehu

 

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A jawabin da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu, ya saki ranar Laraba, ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin Buhari da Tinubu musamman wajen ganin cigaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

A cewar Garba Shehu, rahotannin da ake yadawa cewa akwai rashin jituwa tsakanin Buhari da Tinubu, aikin wasu miyagin yan jarida ne.

“Fadar shugaban kasa na son bayyana cewa babu rashin jituwa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da babban amininsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,” cewar Garba Shehu.

“Rahotannin cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugabannin biyu karya ne, aikin wasu miyagun yan jarida ne.”

“Idan Asiwaju ba ya yawan zuwa fadar AsoRock Villa, ai don shi ba Minista bane.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here