Shugaba Buhari ya Umarci Dukkan Ministocinsa da ke Niyyar Takara a Zaben 2023 da su yi Murabus

Daga karshe Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci dukkan ministocinsa da ke da niyyar takara a zaben 2023 su ajiye aikinsu.

Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al’adu ne ya sanar da hakan bayan taron FEC da Shugaba Buhari ya jagoranta a yau Laraba.

Mohammed ya ce Shugaba Buhari ya bawa ministocin wa’adin kwana biyar daga yau su mika murabus dinsu wato kafin ko ranar 16 ga watan Mayu.

FCT, Abuja – Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022, Channels Television ta rahoto.

Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa a Abuja.

Daga cikin ministocin da suka ayyana niyyarsu na takara akwai Rotimi Amaechi (Sufuri), Chris Ngige (Kwadago), Abubakar Malami (Shari’a), Godswill Akpabio (Neja Delta).

Shima hadimin shugaban kasa Tolu Ogunlesi ya tabbatar da umurnin na shugaban kasa ga ministoci masu son yin takara kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce:

“Yanzun nan: Dukkan ministocin fadar Shugaba Buhari da ke son yin takara za su yi murabus kafin ko ranar 16 ga watan Mayun 2022.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here