Buhari ya ce Mutum 69 ne Suka Mutu a Zanga-Zangar EndSars

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce an kashe mutum 69 a zanga-zangar adawa da cin zarafin ‘yan sanda da aka shafe tsawon kwanaki ana yi a kasar.

Ya ce wadanda suka mutun sun hada da farar hula, da jami’an ‘yan sanda da sojoji.

Ita dai kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce a ƙalla mutane 56 ne suka mutu tun fara zanga-zangar, ciki har da masu zanga-zanga 12 da aka kashe a Legas ranar Talata.

Wani rukuni da ya zama jigon shirya zanga-zangar yanzu ya nemi mutane su zauna a gida.

Kungiyar Feminist Coalition mai fafutukar kare hakkin mata, ta shawarci mutane da su bi duk wata dokar hana fita da ka aka sanya a jihohinsu.

Titunan babban birin Najeriya, da Lagos, da cibiyar zanga-zangar, sun yi tsit amma har yanzu akwai sauran fargaba.

An fara zanga-zangar ne a ranar 7 ga Oktoba, kuma matasa da dama sun shiga an yi da su, bisa neman a soke sashen yaki da ‘yan fashi da makami na rundunar ‘yan sandan Najeriya wato SARS.

An soke shashen daga bisani, amma zanga-zangar ta ci gaba duk da haka.

Lamarin ya ƙara ƙazanta bayan harbe-harbin da wasu jami’an sojin kasar suka yi a inda masu zanga-zangar suka taru a Lekki toll gate da ke jihar Legas, abin da ya janyo kasashe da dama na duniya suka tsoma baki a lamarin.

A ranar Alhamis ne shugaban ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi ta talabijin, kana ya buƙaci masu zanga-zangar da su daina, sannan su bai wa gwamnati haɗin kai domin shawo kan matsalolin da suka addabi ƙasar.

Tambayoyin da bai amsa ba

sharhi daga Nduka Orjinmo, BBC News, Abuja

Duk da cewa jawabin ya zo yayin da lamarin ke ci gaba da faruwa akwai mamaki, gwamnati ba ta yi wani ƙarin bayani dangane da wadanda ke da alhakin kisan ba, don haka lamarin na iya ƙara bai wa mutane haushi.

Yawancin mutane na son a yi adalci ne, musamman ga fararen hular da aka hallaka a makwanni biyu da suka gabata.

Da yawa an yarda cewa za a iya kauce wa kisan da a ce gwamnati ta ɗauki wasu matakan, amma sai aka yi amfani da ƙarfin da ya wuce iyaka a kan masu zanga-zangar ta hanyar amfani da jami’an tsaro da har kawo yanzu sun ci gaba da yawo a gari.

Har yanzu ba mu san mutum nawa ne suka mutu a Lekki ba, gurin da ya zama cibiyar zanga-zangar da ta rikiɗe ta zama fagen kashe-kashe.

Gwamnati ba ta ce komai dangane da lamarin da ya faru a wajen, yayin da har kawo yanzu ake ci gaba da samun rahotannin cewa wasu mutane sun ɓata, adadin wadanda suka mutu na iya ƙaruwa a kwanaki masu zuwa.

Bayanan baya-bayan nan.

An ci gaba da ƙone gidajen yari da gine-ginen gwamnati a Legas, da wasu birane na Najeriya, sannan ana kutsawa manyan kantuna ana kwashe kayayyaki.

An kakkafa shingayen binciken ababen hawa a titunan Legas da wasu manyan hanyoyi a ranar Juma’a, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya rawaito.

An saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 sakamakon zanga-zangar, amma gwamnati ta ce za a cire dokar a ranar Assabar daga 8 zuwa 5 na yamma.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here