Shugaba Buhari ya Yaba wa Dakarun Najeriya Kan Yadda Suke Tabbatar da Zaman Lafiya a Kasar 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba wa dakarun kasar kan yadda ya ce suna tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasar, inda ya bukaci ‘yan kasar da su rika alfahari da sojojin.

Mataimaki na musamman ga shugaban a kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana haka a wata sanarwa ta lokacin kaddamar da asusun tallafi na tunawa da ranar ‘yan mazan-jiya, ta 2022, a ranar Litinin, a Abuja.

Ana dai bikin ne na shekara-shekara domin yabawa da irin bajinta da sadaukar da kai da tsofaffin sojojin na Najeriya suka yi a yakin duniya na daya da na biyu da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a wasu kasashe da kuma cikin Najeriyar.

A wurin bikin Shugaban ya yaba wa tsofaffin sojojin da suka sadaukar da kansu wajen kare kasar da duniya, musamman wadanda suka rasa ransu.

Ya ce, ”Kokarin kasarmu tun lokacin da ta samu yancin kai ya gamu da kalubale na tashin hankali na jama’a da yakin basasa da bore da kuma gwagwarmaya da makamai.

”Amma kuma duk da wadannan matsaloli, kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya kuma burin yan kasar na zama tsare na nan daram.

”Kokarin sojojinmu na wanzar da zaman lafiya da kuma matsayinsu a kan hadin kan Najeriya sun taimaka gaya wajen zaman lafiyarmu.” in ji Shugaba Buhari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here