Mutane 4 Sun Mutu a Kaduna Sanadiyyar Rikici Tsakanin Makiyaya da Mutanen Gari

 

Akalla mutum hudu sun mutu, wasu uku sun jikkata a wani rikici tsakanin maakiyaya da mutanen gari.

Rahoto ya bayyana cewa lamarin ya auku ne kan hanyoyin da makiyaya ke wucewa da shanunsu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf.

Gwamnan jahar, Malam Nasiru El-Rufai, ya nuna alhinisa tare da kira ga jama’a su daina ɗaukar doka a hannunsu.

Kaduna – Wani rikici da ya ɓarke tsakanin mutane da fulani makiya ya yi sanadin mutuwar mutum hudu wasu da dama suka jikkata a Jankasa ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jahar Kaduna.

Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne kan wuraren da fulani ke wucewa da shanunsu, wanda daga baya ya zama faɗa da makami a tsakaninsu.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Yace rahoton da jami’an tsaro suka baiwa gwamnati ya nuna cewa ɓangarorin biyu sun gwambza da juna kafin jami’ai su kariso kuma su shawo kan lamarin.

Me rikicin ya haifar?

Mista Aruwan yace bayan arangama tsakanin ɓangarorin biyu an gano cewa mutum huɗu sun mutu, Luka Nelson,Timothy Koni ,Pasi Peter amda George Frances.

Hakanan kuma wasu uku sun jikkata, waɗan da suka haɗa da Daniel Dauda, Extra James da Henry Frances, kuma an garzaya da su asibiti.

Wasu yan bindiga sun kaiwa Fulani hari Hakanan kuma hukumomin tsaro a jahar sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun farmaki Manchok, karamar hukumar Kaura.

Amma jami’an tsaro sun gano cewa an ka wanna harin ne domin ɗaukar fana a kan rikicin da ya faru da farko.

Da yake martani kan lamarin, gwamna El-Rufa’i ya nuna takaicinsa kan rikicin tare da addu’ar Allah ya jikan mamatan.

Gwamna ya kuma yi kira ga mutanen yankin su rungumi doka su daina ɗaukar doka a hannun su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here