Buhari ga ‘Yan Najeriya: Ku Kara Hakuri da mu

Shugaban kasa Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su yi wa gwamnatinsa uzuri idan su na ganin gazawarsa.

Ministan sadarwa da kuma al’adu, Alhaji Lai Mohammed shi ne ya bayyana hakan a madadin shugaban kasa a wurin taron fadi-ra’ayinka a garin Ilorin.

Gwamnatin tarayya ta jaddada kyawawan manufofinta na inganta rayuwar al’umma, su kuma wakilan al’umma sun bayyana ra’ayoyin su Jaridar Leadership ta wallafa cewa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki ‘yan Najeriya wadanda har ya zuwa yanzun basu lashi romon gwamnatinsa ba, da kuma wadanda su ke ganin gazawar gwamnatin, da su yi hakuri.

Ya yi wannan roko a ranar Juma’a a garin Ilorin a wurin taron fadi-ra’ayinka. Taron wanda an yi shi ne saboda zanga-zangar EndSARS da kuma sakamakon da ta haifar.

Ya samu halarcin sarakunan gargajiya, matasa, ma’ikata, ‘yan kasuwa, dalibai, mata’yan kasuwa da sauransu.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta wallafa yadda shugaban kasan ya umurci ministoci da su koma jihohin su, su yi cudanya da mutane don samun karin haske dangane da zanga-zangar ta bangaren mutane da kuma gwamnati. Taron ya samu halarcin Gwamnan jihar Kwara Abdulrazak Abdulrahman, Sarkin Ilorin Sulu Gambari, kakakin majalisar jihar Hon. Yakubu Danladi, Ministan sadarwa da kuma Al’adu Alhaji Lai Mohammed, wanda shi ne ya wakilci shugaban kasa kuma ya gabatar da jawabi a madadinsa.

“Gwamnatin Buhari ta yi abubuwa masu dumbin yawa domin inganta rayuwar matasa da kuma daukacin al’umma, duk da kuncin tattalin arziki da kasar ta ke fuskanta.

Idan kokarin da mu ke yi bai kai gareku ba ko kuma kuna ganin gazawarmu, muna rokon ku da ku kara hakuri.

“A yanzun haka mun ware naira biliyan 75 na tallafawa matasa don kawar da talauci.” In ji Lai Mohammed. Ministan ya lissafo tsare-tsare makamanci wannan irin su N-Power wanda duk manufar don inganta rayuwar al’umma ne.

Gwamnan Jihar da Sarkin Ilorin sun nuna goyon bayan su ga wannan taro sun kuma tofa albarkacin bakin su.

Sarkin ya yi tsokaci a kan illar yajin aikin kungiyar malaman jami’a (ASUU) a kan ‘ya’yan talakawa wadanda ba su da gatan fita kasashen waje don yin karatu.

Shi kuwa shugaban ASUU na jami’ar Ilorin Farfesa Moyosore Ajao, ya rinjayar da sababin zanga-zangar a kan dadewa da dalibai suka yi a gida su na zaman banza.

Don haka ya yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen wannan yajin aiki.

Sauran wakilan jama’a a wurin taron sun bukaci a bude iyakokin kasa don magance yunwa. Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbata tallafin su na isa zuwa ga talaka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here