Gwamna Matawalle ya Bukaci Hukumar EFCC da ta Binciki Ministocin Buhari
Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya bukaci Hukumar EFCC da ke yaƙi da rashawa ta soma bincikenta da jami’an gwamnatin Buhari da ministocinta, da zaran an sauka daga mulki.
Read Also:
Jaridar Daily Trust ta rawaito Matawalle na wadannan kalamai a matsayin martani kan sanarwar shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa da ke cewa sun turawa gwamnonin da ke barin mulki da kwamishinoni gayyata da zaran sun kammala miƙa mulki, domin bincikensu.
Gwamnan ya ce irin wannan bincike bai kamata ya tsaya a kan gwamnoni da kwamishinoni ba, ya kamata a hada da masu aiki a fadar shugaban kasa.
Matawalle ya kuma shawarci EFCC ta tabbatar ba ta sa siyasa ko son rai a bincikenta ba, domin hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Gwamnan na Zamfara na daga cikin gwamnonin da suka karbi wasikar da EFCC ta aikewa gwamnoni na bincikersu da zaran sun sauka daga mulki