Lamidi Apapa ya Musanta Zargin ƙarbar N500m Domin kawo cikas ga ƙarar da LP ta Shigar a Kotun Sauraron ƙararrakin Zaɓen Shugaban ƙasa

 

Gaskiya ta fito dangane da batun cika aljihun shugaban tsagin jam’iyyar Labour Party, Lamidi Apapa, da N500m.

Apapa ya fito fili ya musanta cewa ya ƙarbi waɗannan kuɗin domin haddasa fitina a jam’iyyar Labour Party.

Shugaban jam’iyyar ya kuma buƙaci Peter Obi, da ya sanya baki domin kawo ƙarshen rikicin shugabancin jam’iyyar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Abuja- Shugaban tsagin jam’iyyar Labour Party, Lamidi Apapa, ya musanta zargin ƙarbar N500m domin kawo cikas ga ƙarar da jam’iyyar ta shigar a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Apapa ya kuma buƙaci ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairru, da ya sanya bakin kan rikicin shugabancin jam’iyyar, domin kawo ƙarshensa, cewar rahoton Daily Trust.

Da ya ke magana da manema labarai, bayan ya sha da ƙyar a hannun fusatattun matasa a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, Apapa ya musanta cewa ya ƙarbi kuɗi da batun wani ko wasu ne ke ingiza shi ya ke ƙoƙarin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.

Ya bayyana cewa dole ne Peter Obi, ya cire son rai ya sanya idon basira wajen magance rikicin domin shawo kan matsalar shugabancin jam’iyyar, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Lamidi ya bayyana laifin Peter Obi

Lamidi ya ce da tuni an manta da rikicin shugabancin jam’iyyar, da ace Peter Obi ya mutunta umurnin babbar kotun tarayya da ke a birnin tarayya Abuja.

Babbar kotun tarayya a Abuja, ta umurci Julius Abure da wasu mutum uku daga kiran kan su a matsayin shugabannin jam’iyyar, bisa samun su dumu-dumu da laifi.

Ya ce kuskure ne Obi ya riƙa mutunta Abure, bayan hukuncin da kotun ta yi, a matsayinsa na ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda ya ke neman a yi masa adalci a gaban kotu.

cheap guest posting

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here