Akwai Bukatar a Amshi Tubabbun ‘Yan Boko Haram – Babakura Abba-Jato

 

Gwamnatin jahar Borno ta kaddamar da fara shirin canza yan ƙungiyar Boko Haram da suka miƙa wuya.

Kwamishinan labaru, Abba Jato, yace ya zama wajibi a karbi masu mika wuyan domin mafi yawansu mata ne da ƙananan yara.

Gwamnatin jahar ta kaddamar da shirin ne a fadar mai martaba shehun Borno, ranar Laraba a Maiduguri.

Borno – Gwamnatin jahar Borno ta ƙaddamar da shirin sulhu da canza mayakan Boko Haram da suka miƙa wuya, kamar yadda daily nigerian ta rawaito.

Shirin wanda ƙungiyar tarayyar turai, EU, ta ɗauki nauyi tare da taimakon kungiyar UNICEF, UND da kuma IMO.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da fara shirin a fadar mai martaba shehun Borno ranar Laraba a Maiduguri, Kwamishinan yaɗa labarai, Babakura Abba-Jato, yace akwai bukatar a amshi tubabbun yan Boko Haram.

A cewar kwamishinan cikinsu akwai mata da ƙananan yara, waɗanda yan ta’addan suka tilastawa zama a jeji, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Yan Boko Haram nawa suka mika wuya zuwa yanzu?

Abba Jato ya bayyana cewa mafi yawacin mutum 6,000 da suka miƙa wuya mata ne da yara kanana, sai kuma wasu mutane da yan ta’addan suka kwace yankunan su kuma suka tilasta musu zama suna musu noma.

Kwamishinan yace:

“Hakanan kuma akwai mayaƙan da suka ɗauki makami a baya cikin waɗanda suka mika wuya ga hukumomi.” Ya bayyana cewa a halin yanzu, ma’aikatar harkokin mata ita ke jagorantar shirin da ya ƙunshi mata da ƙananan yara.

Muna bukatar goyon bayan sarakunan gargajiya – UNICEF

A jawabinta, shugabar ofishin UNICEF a Maiduguri, Phuong Nguyen, ta jaddada bukatar goyon bayan iyayen ƙasa wato sarakunan gargajiya a wannan shirin.

shehun Borno) domin ƙara neman goyon bayanku yayin da gwamnatin jaha ta fara shirin canza ƙananan yara, waɗanda suke da alaƙa da ƙungiyar yan ta’adda.”

“Ranka ya daɗe, waɗannan yaran mu ne, maƙotanmu, da kuma yan uwan mu maza da mata, waɗanda yan ta’adda suka kama lokaci daban-daban yayin rikici.”

“Mafi yawancinsu sun rayu ne a wuraren da yan ta’adda suka kwace, suka maida su tamkar bayinsu, waɗanda suke musu hidima kala daban-daban.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here