Abinda Buratai ya Sanar da Kwamandojinsa a Taronsu na Ranar Litinin
Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Buratai, ya umarci sojoji da su tabbatar da zaman lafiya a Najeriya
Read Also:
Ya sanar da hakan ne a wani taro da yayi da manyan shugabannin sojojin kasa a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba a Abuja – Ya kara da cewa, akwai bata-gari da dama da suke jiran karamin rikici ya auku don su rurar da wutar tashin hankali Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Buratai, ya yi wani taro da manyan shugabannin rundunar soji, duk wasu GOC da kwamandojin filin daga. Kamar yadda The Nation suka tattaro bayanai akan taron da akayi a hedkwatar tsaro a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba. Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Buratai ya ce wa manyan jami’an soji su tabbatar sun zama masu juriya, don hargitsa Najeriya ba nasu bane.
Ya ce wajibi ne sojojin Najeriya su tabbatar da sun samar da kwanciyar hankali a kasa, don mulkin farar hula ne yafi kowanne salon mulki samar da zaman lafiya a Najeriya. Ya kara da cewa, “Ba za mu bari wasu mutane su yi amfani da karfinsu wurin raba mana kasa ba, ko kuma su rura mana wutar tashin hankali ba.” Buratai ya ce ba zai bayar da wata dama da wani zai ci amanar kasa ba. Kuma ya umarcesu da su tabbatar sun sanar da na kasa dasu. Ya ce daga ganin wannan zangar-zangar EndSARS din, bata-gari na samun dama za su yi kokarin raba Najeriya. Yace yana sane da shirin wasu mutane na hada tuggun tayar da hankula, shiyasa suka dauki matakan da suka dace.