Matar Aure ta Tsinke Mazakutar Mijinta
Matar aure a yankin Appawa da ke karamar hukumar Lau ta jihar taraba ta tsinke mazakutar mijinta.
Read Also:
Kamar yadda makwabtansa suka tabbatar, da sanyin asubahi suka shiga cetonsa bayan ihunsa da ya tashesu – Matar ta tabbatar da cewa ta yi hakan ne saboda dirkawa wata budurwa ciki da yayi bayan ita ko haihuwa bata yi ba Wata mata mai matsakaicin shekaru ta tsinke mazakutar mijinta a kan zarginsa da dirkawa wata budurwa ciki a yankin Appawa, wani bangare na karamar hukumar Lau na jihar Taraba. Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa, mijin mai suna Babangida wanda aka fi sani da Bangis yana cikin shekarunsa na 30. Ya samu miyagun raunika a mazakutarsa bayan da matarsa ta yi yunkurin tsinka masa mazakutar a ranar Lahadi.
Wata majiya daga yankin wacce ta sanar da The Nation, ta ce Bangis ya je kasuwa, bayan wahalar da ya sha sai ya isa gida inda ya kwanta bacci. “Da asubahi, matarsa ta tsinke masa mazakuta saboda dirkawa wata mata ciki da yayi. Ya mayar da martani inda ya raunata ta da wukar da ya karbe a hannunta. “Makwabta sun ji ihunsu inda suka garzaya cikin gidan tare da tarar da wannan lamarin,” majiyar tace. A lokacin da aka bukaci sanin dalilinta na kokarin tsinke masa mazakuta, matar ta yi martanin cewa ko a littafin bibul an bukaci a tsinke duk abinda zai sa a yi zunibi. An mika Bangis asibiti kuma na gano cewa har a halin yanzu basu da da ko daya da matar.