‘Yan Sanda Sun Damke Mutune a Jahar Kwara da Cross River
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara da ta Cross River sun cafke mutum 244 a kan zarginsu da sata
Read Also:
Jama’ar suna daga cikin matasan da suka saci kayan gwamnati da na jama’a a yayin zanga-zangar EndSARS – Kamar yadda kwamishinonin ‘yan sandan jihohin suka sanar, an kama wadanda ake zargin da kayan satan Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara a ranar Litinin ta tabbatar da kamen mutum 144 da ke da alaka da satar kayan gwamnati da na jama’a a Ilorin da ke jihar Kwara. Bata-gari da suka boye karkashin inuwar masu zanga-zangar EndSARS a Ilorin a ranar sun dinga satar kayayyakin shaguna da na ma’aikatu. Sun dinga cin zarafin masu ababen hawa da kuma mazauna birnin. A yayin zantawa da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kayode Edbetokun, ya ce sun yi kamen ne bayan kokarin jami’an tsaro na hadin guiwa a jihar, The Nation ta wallafa.
Hakazalika, rundunar ‘yan sandan jihar Cross River ta cafke wasu bata-gari 80 da ake zargi da hannu a cikin lalata kayan gwamnati a tsakanin 23 ga watan Oktoba zuwa 24 ga wata a Calabar. Hukumar ta ce wadanda aka kama sun hada da wadanda suka shiga gidaje da ofisoshin ‘yan majalisu. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an ga masu satar suna kwashe adaidaita sahu da babura. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdulkadir Jimoh, wanda ya zanta da manema labarai a ranar Litinina Calabar ya ce ‘yan sanda sun samo kayayyakin satan, The Nation ta wallafa.