Wani Daga Cikin Bursunonin da Suka Tsere an Sake Kama Shi Da Laifin Kisan Kai

Bayan fursunoni da dama sun tsere daga gidajen gyaran hali da ke Oko da Benin lokacin zanga-zangar EndSARS.

‘Yan sanda sun kara kama daya daga cikin fursinan sakamakon laifin kisa da ya aikata – Dama ‘yan sandan sun kama wasu 10 daga cikin fursinonin sun yi fashi da makamai, wasu kuma kisa ‘Yan sanda sun samu nasarar damkar daya daga cikin fursinoni 1,993 da suka gudu daga gidan gyaran halin Oko da Benin, sakamakon kashe wani da yayi.

The Cable ta ruwaito yadda fursinoni suka gudu sakamakon rikicin zanga-zangar EndSARS. Yayin da suka jera wadanda ake zargin masu laifi ne guda 126 a ranar Laraba, Babatunde Kokumo, kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya ce 10 daga cikinsu fursinoni ne da suka tsere.

A cewarsa, “Mun zage damtse wurin neman masu laifi. Kuma ina so kusan cewa yanzu haka mun samu nasarar damkar 10 daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyara halin Oko da na Benin. “Daya daga cikin fursunonin gidan gyara halin Oko, ya koma kauyensu a ranar don kashe wanda yayi shaidarsa a laifin da ya kai shi ga shiga gidan gyaran halin. “Wasu 3 daga cikinsu kuma sun je yin kwacen wata mota kirar Lexus, yayin da ‘yan sanda suka damkesu.”

A cewarsa, “Wasu biyu sun sace wata mota kirar Toyota. Kuma dama a gidan gyaran halin suka hadu. Rundunar ‘yan sanda da ke Okada, jihar Edo ne suka kama su. Yanzu haka su 10 kenan aka kama. “An samu nasarar amsar bindigogi daga hannun ‘yan ta’addan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here