Kaduna: Gwamnatin ta yi Karin Haske Kan Jiragen Sojoji da ke Shawagi a Jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi ƙarin haske game da jiragen sojoji masu saukan ungulu da ke yawo sararin samaniyar jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya ce sojoji ne da ke yaƙi da ƴan bindiga ke sintiri – Ya yi kira ga al’ummar jihar su kwantar da hankulansu kana suyi watsi da wadanda ke yaɗa jita-jita don tada hankulan al’umma Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce jirage masu saukan ungulu da ake gani suna shawagi a sararin samaniyar jihar farautar ƴan bindiga suke yi. An samu hare-haren ƴan bindigan a wasu sassan jihar a watannin da suka gabata a Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce mutane su kwantar da hankulansu “kan jiragen sojojin” don suna ƙoƙarin tsare mutanen jihar ne.

“Gwamnatin jihar Kaduna ta ce babu buƙatar mutane su tada hankulansu saboda jiragen sojojin da ke shawagi a sararin samaniyar Kaduna,” inji sanarwar.”Jiragen masu saukan ungulu da wasu jiragen jami’an tsaro ne da ke yaƙi da ƴan bindiga a wurare da dama a jihar.

“Gwamnatin Kaduna ta ce kada mutane su tada hankulan su game da jiragen saman sojojin da ke yawo a Kaduna,” inji sanarwar.
Gwamnatin ta yi kira ga ƴan jihar su yi watsi da masu yaɗa labaran ƙarya kuma ta mika godiyar ta ga dukkan hukumomin tsaro da ke bada gudunmawarsu don samar da zaman lafiya a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here