Buhari ya Jinjina wa Matasan Borno

Matasan Borno sun sha jinjina daga wajen shugaba Buhari kan yadda suka kama kansu yayinda sauran mutane ke ta sace-sace da lalata kayayyaki a sauran jihohi.

Gwamnan jihar, Babagana Zulum, shima ya yi alfahari da matasan wadanda suka kwantar da hankalinsu a yayin zanga-zagar EndSARS a kasar – Ku tuna cewa zanga-zangar EndSARS wacce ta fara cikin lumana ta koma rikici bayan wasu bata gari sun janye ragamar ta, sun yi ta lalata kayan gwamnati da na mutane Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma matasan Borno, kan kin shiga sahun masu barnar kaya da sace-sace sakamakon zanga-zangar EndSARS da aka yi a kasar.

Karamin ministan noma, Alhaji Buba Shehuri ne ya bayyana hakan, inda ya ce Buhari ya jinjinawa matasan a wani sakon fatan alkhairi zuwa ga kungiyar masu ruwa da tsaki na zaman lafiya a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, a Maiduguri.

A cewarsa, Buhari na matukar alfahari da matasan Borno wadanda suka nuna halin dattako da nagarta ta hanyar kin shiga rikicin karkashin fakewa da zanga-zangar EndSARS, PM News ta ruwaito.
Ya ce Shugaban kasar ya kuma jinjinawa gwamnan Borno, Babagana Zulum, da sauran masu ruwa da tsaki kan rawar ganin da suka taka wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar. Buba-Shehuri ya nuna irin alfaharin da yake yi da Zulum wanda ya tabbatar da ganin cewa an raba kayan tallafin korona da sauran kayan agaji ga mutane a jihar.

Ya ce: “Shugaban kasar ya yi farin ciki da jajircewar gwamnan da gudunmawarsa wajen yaki da ta’addanci, aikin taimakawa jama’a, mayar da yan gudun hijira muhallinsu da sauran tsare-tsare.”

Da yake nasa jawabin, Shehun Borno, Abubakar Umar-Garbai Ibn El-Kanemi, ya yi godiya ga matasan a kan kwantar da hankalinsu da sukayi da kuma kin shiga zanga-zangar. A nashi martanin, Zulum ya jaddada jajircewarsa ga shugabanci nagari da kuma jinjinawa matasan a kan kame kansu da suka yi a wannan lokaci da ake ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here