Bikin Maulud: Abubuwan da Buhari ya Faɗa wa ‘Yan Nigeria

Yayinda Najeriya ke bikin haihuwar annabi Muhammadu a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga yan Najeria kan wasu muhimman batutuwa.

Buhari ya ja hankalin al’umman kasar a cikin sakonsa na rana wannan rana ta Maulidi – Sakon Shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Garba Shehu, babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai.

1. Ku nuna kauna da fahimta ga sauran yan uwanku ‘yan kasa

Shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su amfani da wannan biki wajen koyi da kyawawan halayen annabi Muhammadu (SAW) ta hanyar nuna kauna da fahimta ga al’umman kasar.
Ya kuma bukaci su bayyanar da kyawawan halayensa na hakuri, gaskiya, rikon amana da mutunci ga kowa.

2. Sako zuwa ga matasan Najeriya

Da yake misali da yawan rikice-rikice da sace-sace da aka fuskanta a fadin kasar bayan wasu bata gari sun janye zanga-zangar EndSARS, Shugaba Buhari ya bukaci matasan Najeriya da su “yi watsi da duk wasu munanan halayya”.

3. Za a hukunta wadanda suka yi sace-sace

Shugaba Buhari ya sha alwashin tabbatar da hukunta dukkanin wadanda ke da hannu a sace-sacen kayayyakin gwamnati da na mutane masu zaman kansu a fadin kasar.

4. Hukunta azzaluman jami’an yan sanda

Buhari ya kuma tabbatar da cika alkawarinsa na yin adalci ga duk wanda jami’in ‘yan sanda suka zalinta.

5. Gargadi a kan annobar korona

Kan annobar korona, Shugaba Buhari ya bayyana cewa zuwa yanzu Najeriya ta yi nasarar magance matsalar ta hanyar tabbatar da adadin mutanen ya yi kasa. Ya kuma shawarci duk ‘yan Najeriya da su kiyaye dokokin kamuwa daga cutar COVID-19, kamar wanke hannaye, saka takunkumi da dokar nesa-nesa da juna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here