WTO: Dalilan da Yasa Amurka Bata Goyen Bayan Ngozi Okojo Iweala

Amurka ta fito karara ta nuna ba ta goyon bayan Ngozi Okonjo-Iweala a WTO

Gwamnatin Trump ta fi karkata wajen Ministar kasar Koriya, Yoo Myung-hee – Okonjo-Iweala ta yi aiki a bankin Duniya, akidunta sun sha ban-bam da Trump Yayin da kafar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala daya ta ke kan kujerar kungiyar WTO, kasar Amurka ta fito ta nuna adawarta ga mutumiyar Najeriyar.

Gwamnatin kasar Amurka ba ta tare da Ngozi Okonjo-Iweala, ta na goyon bayan Yoo Myung-hee ne a zaben wannan kungiya ta kasuwancin Duniya. Kungiyar EU da takwararta AU ta Afrika da sauran manyan kasashen Duniya su na goyon bayan Okonjo-Iweala, Amurka ce kurum babban kalubalanta. Wasu na ganin cewa Amurka ta na yi wa Yoo Myung-hee sha’awar wannnan kujera ne saboda kokarinta da aka gani a gwamnatin Koriya ta Kudu.

Yoo Myung-hee ta na da kyakkyawar alaka da gwamnatin Amurka a karkashin Donald Trump. Kasar Amurka ta ce ta na goyon bayan Yoo Myung-hee ta rike wannan kujera ne domin rikakkar masaniya ce a kan sha’anin kasuwanci a Duniya.

Amurka ta ce Myung-hee ta nuna hakan a shekaru 25 da ta yi ta na aiki. Jaridar Premium Times ta ce ma’aikatar kasuwancin kasar ta bayyana wannan. A ra’ayin mahukuntan Amurka, Ministar Koriyar ta cancanci ta ja ragamar WTO domin ta na da duk abin da ake bukata na zama shugabar kungiyar.

Jawabin ya ce: “Wannan mawuyacin lokaci ne ga kungiyar WTO da harkar kasuwancin Duniya.”

Ko da Amurka ba ta yi magana kan Okonjo-Iweala ba, ta nuna ta fi karkata a kan wanda ta ce ta san aiki. Amma ita ma ‘yar Najeriyar ba kanwar lasa ba ce. Dr. Okonjo-Iweala ta yi karatu ne a manyan jami’oin Duniya, kuma ita ce macen farko da ta fara zama Ministar tattalin Najeriya, ta rike matsayin sau biyu. Ana tunanin akidar Okonjo-Iweala da ta yi aiki a bankin Duniya, ba za ta zo daya da ta Donald Trump wanda ya ke zargin kungiyar WTO da fifita kasar Sin ba.
Kasashen Turai ba su tare da Yoo Myung-hee, wanda gwamnatin Amurka ta ke mara wa baya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here