‘Yan Burtaniya Sun Koka Kan ƙaruwar Farashin Gas

 

Sakataren kasuwanci na Birtaniya Kwasi Kwarteng yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki a masana’antar makamashi game da hauhawar farashin gas.

Tuni wasu kananan kamfanonin makamashi biyar suka durkushe sanadiyyar kasa jurewa hauhawar kashi saba’in cikin ɗari a watan Agusta kawai.

Farashin da gwamnati ta sanya yana hana kamfanonin shiryawa da kwastomominsu.

Yanzu haka matsalar ta fara janyo karancin abinci.

Kamfanonin taki biyu da ke samar da kusan kashi sittin cikin dari na iskar carbon dioxide na Biritaniya sun rufe saboda tsadar iskar gas din.

Nick Allen, babban jami’in kungiyar masu sarrafa nama ta Burtaniya, ya ce nama na iya bacewa a manyan kantunan Burtaniya a cikin makonni biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here