Sabon Hari: Kungiyar ISIS ta Kashe ‘Yan Taliban 45 a Harin da ta kai Afghanistan

 

Kungiyar ISIS ta yi ikirarin kai hare-hare na farko a Afghanistan waɗanda aka kai wa Taliban tun bayan da ta karbi mulkin kasar a watan Agusta.

Kungiyar reshen Afghanistan ta ce ta kai hare-haren guda bakwai a Jalalabad a ranakun Asabar da Lahadi, abun da ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun Taiban 45, da raunata wasu da dama.

Wani shaida ya ce ya ga lokacin da ake kai ‘yan Taliban da dama da suka jikkata asibiti.

Birnin wanda ke gabashin Afghanistan ya kasance wata durka ta kungiyar ISIS.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here