2023: Cancanta ce ya Kamata ta Zama Abar Dubawa a Zaben Gaba – Sanata Malam Ibrahim Shekarau

Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce babu tsarin kama-kama a mulkin kasa kundi tsarin mulkin APC.

Tsohon gwamnan kuma sanata Kano ta tsakiya ya ce cancanta ce ya kamata ta zama abar dubawa a zaben gaba.

Shekarau ya yi tsokaci akan alakar da ke tsakaninsa da gwaman Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamna Kwankwaso.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce babu wani tsarin karɓa-karɓa a kundin tsarin gudanarwa na jami’iyyar APC.

Sanatan, ya yi kira da masu kaɗa ƙuri’a da su mayar da hankalinsu kan ɗan takarar da ya cancanta maimakon tsarin shiyya-shiyya.

A cewar Malam Shekarau, ingancin ɗan takara shine ya kamata ya zama muhimmin abin dubawa a zaɓe mai zuwa, ya ƙara da cewa babu wani tsarin karɓa-karɓa cikin jam’iyyar APC face kawai tunani ne da mutane suke ganin hakan ya dace.

“Ina so na gaya muku cewa a kundin gudanarwa na APC, babu wurin da aka ambaci maganar bayar da mulki na shiyya-shiyya. Ina ga dai jam’iyyar PDP ce kawai ke da wannan tunanin.

“Abinda kawai muka sani shine ingancin shugabanci da adalci tare da tafiya da kowa; wannan shine kawai.” In ji Shekarau.

Bugu da ƙari, Shekarau ya jaddada cewa alaƙarsa da tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso, da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na nan kalau.

Ya ce, “Ni da Ganduje muna tare tsawon shekaru. Lokacin ina famanat sakatare shi kuma lokacin yana Kwamishina, tun can muna mu’amala tare.

“Haka abin yake ni da Kwankwaso; bambancin siyasar mu bai shafi alaƙar mu ba ko kaɗan kuma ban taɓa barin wata jam’iyya zuwa wata ba saboda shi” cewar Malam Ibrahim Shekarau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here