Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda ake Zargi da Yin Tarzoma

 

‘Yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da tada tarzoma a Zamfara a yau Lahadi.

Tarzomar ta kai ga lalata dukiya da ya hada da lalata wani bangare na fadar Sarkin Shinkafi.

‘Yan sandan sun yi kira ga jama’a da su kula da ‘ya’yansu ko yaushe dan guje wa rigima.

Rundunar ‘yan sanda a Zamfara ta kame mutane 18 da ake zargi a kan wani rikici, wanda ya kai ga lalata dukiya ciki har da fadar Sarkin Shinkafi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya fitar a ranar Lahadi a Gusau.

Matasa dauke da bindigogin dane, adduna da sanduna sun lalata fadar Sarkin Shinkafi da wasu gidaje biyu a garin Shinkafi.

“Hadaddiyar rundunar‘ yan sanda da ta sojoji sun mayar da martani cikin sauri kuma sun tarwatsa masu zanga-zangar don kauce wa rusa doka da oda da yiwuwar asarar rayuka da dukiyoyi.

“Mutum 18 da ake zargi da aka kame a yanzu haka suna hannun‘ yan sanda ana yi musu tambayoyi.

Shehu ya ce “Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Abutu Yaro ya umarci CID na jihar da su fara gudanar da bincike a kan zanga-zangar ba bisa ka’ida ba da nufin gano yadda lamarin ya faru.”

Yaro ya gargadi iyaye da masu kula da su kula da ‘ya’yansu ko yaushe don hana su shiga cikin ayyukan ta’addanci. (NAN)

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here