Matsalolin da Aka Dauko Daga 2020 Zasu Cigaba da Fama a 2021
A ranar Juma’ar nan aka shiga sabuwar shekara a Najeriya da wasu kasashe.
Akwai matsalolin da aka kinkimo daga 2020 wanda za a cigaba da fama da su.
Wadannan kalubale sun hada da satar mutane da ake yi har sai an biya fansa.
A lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara a Najeriya, akwai jerin matsalolin da su ka addabi kasar da har yanzu ba a iya shawo karshensu ba.
Daga cikin abubuwan da su ka dabaibaye Najeriya akwai rikicin Boko Haram, garkuwa da mutane, tsadar kayan abinci, zanga-zanga, da siyasar 2023.
Jaridar Vanguard ta tattaro wadannan matsaloli na 2021, mun tsakuro maku wasu daga cikinsu:
1. Tattalin arziki
Duk da alkaluma sun tabbatar da karfin GDP, tattalin Najeriya ya na fuskantar kalubale da bashi. Sannan an gaza shawo kan darajar Naira, farashin mai bai tashi sosai a kasuwar Duniya ba.
2. Tsadar kayan abinci
Read Also:
Ana fama da matsalar tashin farashin kaya musamman kayan abinci wanda ake ganin zai sauka a 2021.
An bude iyakoki a 2020, amma ba a bada damar shigo da abinci daga kasashen waje ba.
3. Rashin tsaro
Wata babbar matsala har a shekarar nan ita ce ta rashin tsaro inda ake fama da rikicin Boko Haram, garkuwa da mutane, rigimar makiyaya da manoma da hare-haren ‘yan bindiga.
4. Zanga-zanga
A shekarar bara an yi ta fama da zanga-zanga iri-iri wanda su ka hada da #EndSARS, #SecureNorth da sauransu. Akwai yiwuwar har a 2021, a cigaba da irin wannan fafutuka.
5. Siyasar 2023
A wannan shekara ta 2021, manyan ‘yan siyasa na jam’iyyun APC da PDP za su cigaba da kokarin wanke allunan siyasarsu domin su shiryawa babban zabe mai zuwa da za ayi a 2023.
6. COVID-19
Annobar Coronavirus ta na cikin matsalolin da za a cigaba da fama da su. A dalilin wannan cuta ake sa takunkumi, aka hana mutane fita neman na abinci da yin ibada da sauran taro.