Na Kasance Mai Biyayya ga Aikin Gwamnati da Kiyaye Dokoki – Kingsley Moghalu

An nada Farfesa Kingsley Moghalu sarautar Nwewi ta “Ifek’ego Nnewi”.

Moghalu ya bayyana biyayyarsa ga aikin gwamnati da kiyaye dokoki.

Ya bayyana nada shi sarautar a matsayin bashi kwarin gwiwa na ci gaba da aiki tukuru.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma dan takarar shugaban kasa na Matasan Cigaban Party (YPP) a zaben 2019, Farfesa Kingsley Moghalu, an ba shi sarautar masarautar Nnewi ta “Ifek’ego Nnewi” (Mafi girma fiye da kudi) daga Igwe na Nnewi, HRH Dr Kenneth Orizu III, Daily Trust ta ruwaito.

Sarkin masarautar ne ya ba shi sarautar a wani kayataccen biki a Nnewi yayin bikin Igwe Orizu na shekara-shekara na Ofala karo na 57.

Tare da wannan sarautar, Moghalu yanzu mamba ne na shahararriyar kungiyar Manyan Sarakunan Nnewi, ɗaya daga cikin garuruwan kasuwanci mafi karfi a Najeriya.

A wani sanarwa da ya fitar jiya yace: “Sabon taken nawa sanarwa ce mai karfi na dabi’u a rayuwa. Mutunci ya fi kuɗi. A hidimtawa jama’a ga duniya da kasata, ban taba saba doka ba. Yana da mahimmanci abin da muke koya wa al’ummarmu da yadda ake tuna mu.

“Sarautar ta zama mai mahimmanci saboda basaraken gargajiyar ya nuna godiya ga irin gudummawar da nake baiwa mahaifata. Wannan yana karfafa min gwiwa in ci gaba da bin turbar aiki, ”in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here