Babban Bankin Najeriya ya yi Gargaɗi Kan Yin liƙi da Kudi a Lokacin Biki
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jaddada gargaɗinsa ga jama’a a kan yin liƙi da takardar kuɗin ƙasar ta Naira a lokacin biki.
A sanarwar da hukumar bankin ta fitar ta Twitter ta ce, saɓa wa dokar bankin ta 2007 laifi ne da zai sa a ci tarar mutum naira dubu 50 ko kuma ɗaurin gidan yari da bai wuce wata shida ba ko kuma duka biyu.
Read Also:
Wasu ‘yan Najeriya suna da al’adar yin abubuwa kamar su kek da takardar kuɗin ƙasar ta Naira domin aika wa ‘yan uwa da masoya a lokacin bikin ranar haihuwa ko kuma wani biki na aure da makamantansu.
Haka kuma sukan yi liƙi da takardar ta Naira a lokacin bukukuwa.
Laifukan da bankin ya zayyana da ake yi da takardar kuɗin sun haɗa da, liƙi da sayarwa da cukuikuyewa da rubutu ko zane ko tattaka su ko rawa a kansu da sauransu.
Babban Bankin na Najeriya ya fitar da wannan gargaɗi ne a daidai lokacin da takardar kuɗin ke ƙaranci sakamakon canjin takardar naira ta 200 da 500 da kuma 1,000 da bankin ya yi.